15/06/2025
TARIHIN YAKIN BIYAFARA, ZA KU JI ABUBUWAN DA BAKU TABA JI BA A YAKIN BIYAFARA. KASHI NA DAYA.
Wani kundin asiri na difilomasiyya mai shafuka dubu 21 da Amurka ta fitar, ya zo da wasu Batutuwa Da Su ka Shafi basasan Nijeriya daga 1967 zuwa 1970 wadanda kuma ba taba jinsu ba a baya.
A safiyar ranar litinin din 1 ga Yulin 1967 matashin Shugaban kasar Nijeriya na lokacin, Janar Yakubu Gowon ya kasance cikin halin dimuwa a ofishinsa dake babban hedikwatar sojojin Nijeriya, wato barikin Dodan, a Legas. Dalilin dimuwar tasa kuwa shi ne matsin lambar da yake fama da shi, kan cewa lallai-ilalla ya bayar da izinin kai mamaya kan sabuwar Jamhuriyar Biafra da ta b***e daga Nijeriya. A dai-dai wannan lokacin kuma manyan Jami’an sojan da aka tura kasashen wajen don samun horo, duk an maido da su gida. Jiragen kasa daga Kaduna da Kano kuma dauke da lodin sojoji da kayan aikinsu sun nausa tsallaken kogin Binuwai daga ta Kudu a karkashin jagorancin Kanar Muhammad Shuwa (yanzu marigayi) inda s**a yi sansani a Makurdi.
Kafin nan motsawar rundunar Kanar Shuwa, an rigaya an jibge bataliya ta biyu a garin Adikpo. Bataliya ta hudu kuma a karkashin Manjo Sule Apollo, ta sauka a garin Oturko cikin shirin kafsa yaki. A dai wannan ranar, Manjo B.M. Usman, daya daga na hannun daman Janar Gowon, ya shaidawa Jami’in kula da lamurran soja a ofishin jakadancin Amurka dake Nijeriya cewa: “Na ma rasa abin da (Janar Gowon din) ke jira; domin mazaje dai sun riga sun shirya, kuma sun kagara da yaki.
Kalaminsa na umarni kadai suke jira.”Kazalika su ma mambobin majalisar koli ta mulkin soja, wadanda kan yi ganawa a kullum sau biyu, su maganar Gowon kawai suke jira. A takaice dai, duk kasar ta dauki haramin yaki. Ita ma ballalliyar Jamhuriyar Biafra, ta kimtsa tsaf, tana zaman ko-ta-kwana.
Ranar 27 ga Yuni 1967, Mista Cyprian Ekwensi, mashahurin marubucin adabin nan, wanda a lokacin shi ne babban Daraktan watsa labarai na ’yan-awaren Biafra, ya shiga gidan rediyon Muryar Biafra din, wanda kafin b***ewarsa, sunan sa rediyo Enugu, ya kirayi al’ummar Biafra da cewa su zauna cikin shirin kawo musu mamaya daga sojoji ran 29 ga watan, “Domin Arewa sun saba da kai hari yaki ne ran 29 ga wata.” Wannan maganar tasa kuma shagube ce ga Manjo T.Y. Danjuma, loakcin da ya shugabanci sojojin da s**a kawar da magabacin Janar Gowon, wato Manjo Janar Aguyi-Ironsi, inda aka kashe shi a wani dajin bayan garin birnin Ibadan. A lokacin, Janar Gowon dai shekarunsa na haihuwa 31 ne, amma shi ke da ragamar tafiyar da harkokin al’ummar da ta kai mutum miliyan 57 har na tsawon watanni 10 cur, don haka, lamarin ke da nauyi a gare shi. Shi kuma Cif Obafemi Awolowo na da shekaru 58, a sannan kuma, shi ne amintaccen waziri kuma mashawarcin Gowon din a kan sha’anin harkokin waje; Mista Okoi Arikpo da Mista Philip Asiodu kuma, ko wannensu, yana aiki a ma’aikatan harkokin kasuwanci; da kuma na masana’antu. Dukkan su a matsayin ministocin ko wace ma’aikata.
Su ukun kuma, sun zarga zargen zargo wuyayen manyan kamfanonin mai na Dutch Oil da na Shell-BP, kasantuwar sun yi niyyar daina baiwa gwamnatin tarayyar Nijeriya harajojinsu, da nufin mikawa ga sabuwar gwamnatin ballalliyar Biafra; wadanda kuma sun kai fam dubu 250, daga ran 1 ga watan Yuni 1967 din. Dalili kuwa shi ne Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu, Shugaban ballalliyar Biafra ya umarci kamfanonin biyu da su koma da biyan harajojinsu ga gwamnatin da ke da mazaunin ta a birnin Enugu; in kuma sun ce ba haka ba, to fa za su fuskanci tarar da shallake hankali.
A takaice dai, kuma kai tsaye, abin da hakan ke nufi shi ne Ojukwu ya bukaci kamfanin mai Shell-BP da ya biya gwamnatin shi harajin fam miliyan biyu ne; wannan kuma na nufin hana duk wani jirgin ruwan kasuwanci da na daukan mai tsayawa a tasoshin jiragen ruwan Koko, Warri, Sapele, Escrabos Bonny, Fatakwal, da kuma Kalaba; wadanda Ojukwun ya ayyana da cewa halastattun yankunan ballalliyar kasar Biafra ne, mulkan-kamilan. Yayin da ita kuma gwamnatin Nijeriya ta sarkafa ma kamfanoni takunkumin daina duk wata huldar tattalin arziki da ballaliyar gwamnatin Biafra.Gwari-gwari, Biafra na iko da doron kasa, inda rijiyoyin mai da na’urorin hako shi suke; gwamnatin Nijeriya kuma na iko da gabobin teku da kuma ruwayen teku din, inda jiragen ruwa ke karakainar kaiwa da komowa.