08/05/2026
Kuskure goma (10) da matan aure keyi a gidan miji:
Number (9) da number (10) su ne mafi muni
--------------------------------
1. Tattauna sirrin matsalolin gidan miji da abokai da dangi
A kowane gidan aure ana samun matsaloli, sai dai masu hankali acikin matan aure ke ɓoyewa su bar komai a wurin Allah
--------------------------------
2. Yawan tattauna matsalolin miji da kushe ƙoƙarinsa a gaban 'ya'yansa
Wannan yana sa yara su raina ƙoƙarin da mahaifinsu keyi acikin gida
--------------------------------
3. Cusawa yara ƙiyayyar amaryar mahaifinsu (kishiya)
Watarana za ki iya mutuwa ki bar yara hannun kishiya ko rashin lafiya mai tsanani
--------------------------------
4. Ƙiyayyar yaran kishiya da neman ganin bayansu
Shin ko kin san cewa Allah zai iya ɗaukaka 'ya'yan kishiryarki su zamo manyan mutane masu daraja watarana?
--------------------------------
5. Gasar haihuwar yara domin samun kaso mafi girma acikin gadon dukiyar miji
Shin ko kin san cewa mijinki zai iya talaucewa kamin mutuwarsa?
--------------------------------
6. Tunanin cewa miji zai mutu yabarki da yara acikin wahala
Waye ya sanar dake cewa miji ke fara mutuwa ya bar matarsa? Mata sunfi yawan mutuwa su bar mazajensu sanadiyyar (haihuwa, hawan jini, ciwon sikari, tashin gobara a gida, ƙunar ruwan zafi, da sauransu
Idan ki ka je assibiti, zaki samu mafiyawan masu jinya a (emergency, female wards, da ICU) mata ne da ƙananan yara, ƙalilan ne maza acikinsu.
--------------------------------
7. Kyauta acikin dukiyar miji ba tare da saninsa ba
Dukiyar miji amana ce a gareki, dole ki sanar dashi duk abunda za ki aikata acikin dukiyarsa
Ko baƙo zai shigo gida (mace ko namiji) dole ki sanarda miji domin neman yardarsa da amincewarsa.
--------------------------------
8. Fifita buƙatun naki dangi sama da dangin miji
Yan uwa da dangin miji su ne sukafi kusanci dashi sama da dangin matarsa, kar ki cilasta mijinki yiwa dangin ki ɗawainiyar da baya yiwa nashi dangi.
--------------------------------
9. Rashin godiya da hango ni'imar gidan wasu
Ɗawainiyar gidan aure tana da yawa sosai, sai jarumi acikin maza ke iya ɗaukar nauyin matarsa da yara na tsawo shekaru 10, 20, 30, ko 40
Abinci, sutura, sabulai, magani, ruwan sha, kuɗin lantarki, kuɗin gas, kuɗin makarantar yara, kuɗin transport da kai yara makaranta 🥹🥲
Wallahi duk matar dake raina ƙoƙarin mijinta, ba zatayi ƙarshe mai kyau ba.
--------------------------------
10. Saɓawa miji da goyon bayan yara zuwaga ɓarna
Duk abunda yara ke aikatawa acikin gida, mahaifiyarsu ta san komai
Wasu mata zasu goyi bayan yara zuwaga ɓarna saboda son zuciya irin nasu
- idan miji ya hana yara fita, sai bayan mijin yaje aiki ko kasuwa sai mahaifiyarsu ta basu izinin fita
- idan miji ya hana yara zuwa biki, mahaifiyarsu ta basu izini
- idan miji ya hana yara fita babu hijabi, sai mahaifiyarsu ta basu damar fita da gyale
- idan miji ya hana yara fita yawon banza, ko mu'amala da abokan banza, sai mahaifiyarsu ta basu izini
Idan wani abu ya faru marar kyau, sai mahaifiyarsu tace ƙaddara ce kowa da irin tasa.
Follow for more health tips and awareness ✨️
Daga,
Alhassan mai lafia.