Nutrition Da Hausa

Nutrition Da Hausa 🥗 Ingantattun shawarwarin lafiya da abinci cikin Hausa.
📚 Bayanai bisa hujjojin kimiyya.
👇 Bi shafin don ƙarin ilimi.

04/07/2026

Shin ka taɓa tambayar kanka, wa ake kira Nutritionist?"

Kana bukatar duk wadannan nau'in abincin a kowani wuni, ka daure kasamu akalla guda 4 zuwa 5 acikinsu duk yini, suna da ...
03/07/2026

Kana bukatar duk wadannan nau'in abincin a kowani wuni, ka daure kasamu akalla guda 4 zuwa 5 acikinsu duk yini, suna da matukar muhimmanci ga lafiyar mu.

&_share.

02/07/2026

"Kana cin abinci kullum, amma ka taɓa tambayar kanka me yasa wasu mutane suke da ƙoshin lafiya, wasu kuma suna yawan rashin lafiya duk da suna cin abinci?

Amsar tana cikin Nutrition..."

30/06/2026

"Kana jin ana cewa Nutrition, amma ka san ainihin ma'anarsa?"

A yau bari mu fara daga tushe.

"Nutrition" kokuma ilimin abinci mai gina jiki, fanni ne da ke nazarin yadda abinci da abubuwan da ke cikinsa suke shafar lafiyar É—an Adam.

Ba wai cin abinci kawai ba ne, amma zaɓen abinci mai kyau, yadda jiki ke amfani da shi, da yadda yake taimakawa wajen girma, samar da ƙarfi, da kariya daga cututtuka.

A wannan shafi, za mu tattauna duk abin da ya shafi lafiya da abinci cikin Hausa mai sauƙin fahimta, bisa hujjojin kimiyya.

Idan kana son koyon yadda za ka kula da lafiyarka ta hanyar abinci.

ka bi shafin "Nutrition da Hausa"

29/06/2026
29/06/2026

"Kana ci sau uku a rana, amma ka san mene ne Nutrition?"Gabatarwa.Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake saduwa a shafin Laf...
29/06/2026

"Kana ci sau uku a rana, amma ka san mene ne Nutrition?"

Gabatarwa.
Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake saduwa a shafin Lafiya da Mansoor. A yau za mu fara jerin darussan Nutrition daga tushe, domin kowa ya fahimta.

Ma'anar Nutrition.
Nutrition kalma ce ta Turanci da ke nufin ciyar da jiki ta hanyar samun abinci mai gina jiki da kuma yadda jiki ke amfani da wannan abinci domin ya ba mu kuzari, ya taimaka mana girma, ya gyara ƙwayoyin jiki, kuma ya kare mu daga cututtuka.

A sauƙaƙe.
Nutrition ba wai cin abinci kawai ba ne. Yana nufin cin abincin da ya dace, a adadin da ya dace, kuma a lokacin da ya dace domin jiki ya yi aiki yadda ya kamata.

Misali.
Idan mutum yana cin abinci kullum amma ba ya samun sinadaran da jikinsa ke buƙata, zai iya fuskantar matsalolin lafiya duk da cewa yana cin abinci.

🎯 Muhimmin saƙo.
Saboda haka, abin da ya fi muhimmanci ba yawan abinci ba ne, ingancin abincin da muke ci.

Idan wannan darasin ya amfane ka, ka yi Follow sannan ka yi sharing domin wasu su amfana. A darasi na gaba za mu koyi:

"Wane ne Nutritionist?"

Address

Zuma Rock
Abuja
0

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nutrition Da Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share