18/09/2018
Mata masu yawa a kasar Hausa na zaman aure a cikin gida, ba tare da fita neman aiki a waje ba. Zaman gida na da nasa amfanin, da kuma kalubale. Wannan rubutu zai yi tsokaci ne akan yadda matan dake zaune a gida zasu tafiyar da rayuwa mai ma’ana, musamman a dai-dai wannan lokacin da al-umma take fama da kalubale iri-iri.
1. KI KASAFTA LOKACI: Kafin ki ankara rana ta fadi ba tare da kulla wani abun azo a gani ba, banda nauyin tafiyar da alamuran gida da s**a rataya akanki. Duk da cewa babu takura idan aka kwatanta da wajen aiki, akwai matukar muhimmanci ki tsara duk wasu abubuwa da zaki yi a wannan rana bayan gari ya waye. Aikin sana’arki ne, unguwa zaki je, karatun Al-Qur’ani ne, zaki buga waya ne, zaki kalli wasan kwaikwayo ne, ya zamana komai yana da lokacinsa. Yin haka zai baiwa wannan rana tsari, sannan idan kina da yara, suma zasu fahimci batutuwan da kowace rana ta tanada da lokutan aiwatar da su. Yara suna son rayuwa mai tsari, kuma kema zai amfane ki.
2. KI KULLA ZUMUNCI: Musamman idan kina da sana’a, ko kina zuwa makarantar boko ko addini, ko kuma kina cikin wata ‘yar wata kungiya ne. Ki tabbatar kin kulla zumunci da ‘yan uwanki mata a wadannan harkoki domin tattauna matsalolinku, baiwa juna shawarori, hira domin nishadi da sauraron koken juna. Wannan zai rage zaman kadaici, kuma zai hada dangantaka da sauran mata wadanda rayuwarku ke da alaka. Zasu iya kasancewa iyayen yara a makaranta, abokan karatu a Islamiyya, makota a unguwa da sauransu.
3. KI KWARE WAJEN KASANCEWA UWA MAI DADI: Babu shakka duk iyaye mata suna da dadi, amma zama uwa shi kanshi wani aiki ne mai wahala. Me yaranki suke so? Shin kina kula da lafiyarsu? Kina kai su wuraren da zasu ringa wasa suna jin dadi? Shin jifa-jifa, kina saya musu abinci ko abun sha mai dadi, ko kayan wasa? Kar kiyi shakkar duk wani abu da zai sawwaka wa rayuwarki idan har kin tabbatar kina baiwa ‘ya’yanki tarbiyya mai kyau. Dan adam tara yake bai cika goma ba, saboda haka kar ki bata lokaci wajen tabbatarwa sai komai ya tafi yadda k**e so. Idan har ke da ‘ya’yanki kuna jin dadin rayuwarku, kuma kina iya biya musu bukata, to hakan ya wadatar.
4. KI SAMU MAI TAIMAKA MIKI: Idan kina da hali, to ki samu mai taimako saboda kula da gida da yara kullum, babu dare, babu rana jan aiki ne. Masu hikimar magana s**a ce “hannu daya baya daukar jinka”, saboda haka babu laifi idan kika samu wani mai taimaka miki da tafiyar da harkokin gida. Idan kina da unguwar zuwa, ko wani abun yi a kasuwa, to hankalinki ba zai tashi ba.
5. KI RINGA FITA WAJE: Wannan gaskiya ne. Idan kina da miji, ki tambayi izinin shi ya kyale ki, ki fita ke kadai wani lokacin ba tare da yara ba (idan yaran ba jarirai bane). Ya zamanto zaki iya zuwa wajen kawaye ko ‘yan uwa domin hira, ko ziyara, ko wani abun karin ilimi. Wannan zai kara miki karfin gwiwa, kuma ya bude tunaninki dangane da zaman duniya da rayuwa. Bugu da kari, zaki fahimci aikinki daga waje, yadda idan kin komo gida, zaki tafiyar da nauyin da Allah Ya dora miki yadda ya kamata. Za kuma ki zama kina da alaka da jama’a a waje, wadanda ba lallai bane su san ko mene ne yake tafiya a rayuwarki ta gida. Yin haka na kara nutsuwa da hazaka a zaman gida saboda ba duniya daya kawai k**e da shi ba. Kina da wata rayuwar a waje.
6. KI YI WA KANKI IHISANI: Yaran ki ‘yan kanana baza su baki albashi ba, kuma ba lallai bane su yaba miki a kowace rana. Tunda kuwa babu kudaden shiga, wani lokacin zaki ga kamar ba’a ganin darajar ki, saboda haka kar ki bari hakan ya kashe miki gwiwa. Kiyi wa kanki albashi. Ki ringa yabawa kanki, sannan ya zamanto kin koya wa mijinki da ‘ya’yanki nuna jin dadinsu game da yunkurin da k**e yi musu. Kar ki ji kunyar tambayar lada, ko tsire ko ma atamfa. Idan har mijinki yana da wasu hanyoyi na nuna farin cikinsa, ki gode sannan ki bayyana yadda hakan ya kara miki karfin gwiwa wajen tafiyar da harkokin gida.
7. KI K**A SANA’A: Duk wani hali dama ne. Idan zaman aure k**e a cikin gida, to na tabbata kina da matsala, kuma ‘yan uwanki mata suma suna da irin wannan matsala. Ki kulla zumunci da su, sannan ki fahimci matsalolin dake ci musu tuwo a kwarya. Ke kuma, sai kiyi tunanin hanyar da zaki warware wannan matsala cikin hanzari ba tare da bata musu lokaci ba, kuma ba tare da sun kashe kudi mai yawa ba. Wannan zai zama sana’a, sannan ki nemi kwararru domin karin ilimi yadda zaki inganta ta. Ki tabbatar samun riba ba shine abu mafi muhimmanci ba a farko, har sai sana’ar ta kafu kuma ta samu karbuwa sosai. Ki samar da wani abu da zai sa jama’a su dogara akan ki. Allah Ya albarkaci iyayen mu baki daya.
Ga duk macen dake bukatar fara sana'a, zata iya zuwa shafin Kasuwar Bello tayi rijista, ta fara sayar da kaya.
Maryam Abdullahi Yahaya ta bude shagon man shafawa a www.kasuwarbello.com
Kasuwar Bello, Kasuwar Ku Ce!!!