24/08/2026
Abubuwan Da Suke Hana Mata Daukar Ciki 🤰
Rashin ɗaukar ciki ba lallai yana nufin mace ta yi wani kuskure ba. Akwai dalilai da dama da s**a shafi lafiyar mace da namiji.
Wannan darasi yana taimakawa wajen fahimtar wasu abubuwan da za su iya sawa mace ta rage damar samun ciki.
1️⃣Rashin sanin lokacin fitar ƙwai (Ovulation):- Mace tana da wasu kwanaki a wata da damar ɗaukar ciki ta fi yawa. Rashin sanin wannan lokaci na iya sa ma'aurata su rasa lokacin da damar samun ciki sosai.
2️⃣Rashin kula da Infection ko Cututtuka k**ar Chlamydia, Gonorrhoea da PID na iya haifar da matsala ga bututun mahaifa idan ba a yi maganinsu da wuri ba suna iya hana samun juna biyu.
3️⃣Yin amfani da magunguna ba tare da shawarar ma'aikacin lafiya ba, magunguna na iya shafar hormones ko tsarin fitar ƙwai. Saboda haka, bai k**ata a riƙa shan maganin fertility ko hormone da kai ba.
4️⃣Matsalar nauyin jiki
Kiba mai yawa sosai na iya rikita hormones kuma ya shafi ovulation.
5️⃣Shan taba da wasu abubuwan maye
Waɗannan abubuwa na iya rage lafiyar ƙwayoyin haihuwa kuma su rage damar samun ciki.
6️⃣Rashin kula da matsalar al'ada
Idan al'ada tana yawan rikicewa, ta daina zuwa, ko kuma tana zuwa ba bisa ka'ida ba, yana da kyau a nemi shawarar ma'aikacin lafiya domin a gano dalili.
7️⃣Yin amfani da wasu sinadarai a farji
Yawan amfani da douching ko wasu sinadarai marasa dacewa na iya dagula daidaiton farji kuma ya ƙara haɗarin kamuwa da infection.
8️⃣Idan ma'aurata suna yin jima'i ba tare da kariya ba na tsawon shekara 1 ba tare da samun ciki ba, ya dace su je asibiti ayi musu binciken fertility. Idan mace tana da shekaru 35 ko sama, ana iya neman binciken bayan watanni 6.
Kada a ɗora wa mace laifi kai tsaye idan ba ta samu ciki ba. Matsalar fertility na iya kasancewa daga mace, namiji, ko duka biyun. Saboda haka, binciken ma'auratan biyu ya fi dacewa.
Ya Allah duk wadanda suke neman Haihuwa Allah ka basu masu Albarka kuma ka rayasu bisa Sunna Amin
HILAL PRIMACARE HEALTH SERVICES