SAFMA Natural Herbal Care

SAFMA Natural Herbal Care Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from SAFMA Natural Herbal Care, Medical and health, No. 5 Rahama Road Hayin Dan Mani Kaduna, Kaduna.

CHIKAKKEN BAYANI KAN AMFANI DA TSIRRAI WAJEN WARKAR DA CUTUTTUKA.Amfani da tsirrai wajen magani(Herbal Medicine ko Phyto...
04/08/2026

CHIKAKKEN BAYANI KAN AMFANI DA TSIRRAI WAJEN WARKAR DA CUTUTTUKA.

Amfani da tsirrai wajen magani
(Herbal Medicine ko Phytotherapy) hanya ce da aka daɗe ana amfani da ita tun ƙarni da dama. Tsirrai suna ɗauke da sinadarai na halitta da za su iya taimakawa wajen warkar DA wasu cututtuka ko rage radadin ciwon ko tallafawa jiki. Haka kuma, an samo wasu magungunan zamani ne daga sinadaran tsirrai.

⚡Amfanin tsirrai wajen magani

~Rage kumburi daga ciwo.

~Yaƙi da wasu ƙwayoyin cuta (bacteria da fungi).

~Ƙara ƙarfin garkuwar jiki.

~Taimakawa narkewar abinci.

~ Samun waraka daga tari da mura.

~Taimakawa wajen warkar da hawan jini ko ciwon sugar (Diabetes) a wasu lokuta, amma sai da kulawar ƙwararren ma'aikacin lafiya.

⚡Wasu tsirrai da amfaninsu

Habbatussauda (Black Seed)🕳️: Ana amfani da ita wajen tallafawa garkuwar jiki da rage kumburi.

Citta (Ginger) 🫚: Tana taimakawa rage tashin zuciya, mura, da ciwon makogwaro.

Tafarnuwa (Garlic) 🧄: Tana iya taimakawa lafiyar zuciya da rage wasu ƙwayoyin cuta.

Aloevera 🌱: Ana amfani da ita wajen gyaran fata da kuma taimakawa warkar da ƙananan raunuka.

Moringa (Zogale)🌿: Tana da sinadarai masu gina jiki da bitamin.

⚡Hanyoyin amfani

➡️Tafasa ganye a sha (decoction).

➡️Jiƙa ganye a ruwa (infusion).

➡️Yin garin tsiro a sha ko a haɗa da abinci.

➡️Shafawa a fata idan ya dace da irin tsiron.

⚡Muhimman abubuwan lura

Ba duk tsiro ba ne ke da tabbacin warkar da kowace cuta.
Wasu tsirrai na iya yin illa idan aka sha fiye da kima ko aka haɗa su da magungunan asibiti.

Mata masu juna biyu, masu shayarwa, yara, da masu fama da manyan cututtuka su nemi shawarar likita kafin amfani da magungunan gargajiya.

Idan cuta ta yi tsanani ko ta daɗe ba tare da sauƙi ba, a je asibiti domin cikakken bincike da magani.

⚡Kammalawa

Tsirrai na da muhimmiyar rawa wajen kula da lafiya, kuma binciken kimiyya ya tabbatar da amfanin wasu daga cikinsu. Duk da haka, ya kamata a yi amfani da su cikin ilimi da taka-tsantsan.👌

Burinmu shi ne SAFMA NATURAL HERBAL CARE ta zama babbar cibiyar samar da ingantattun magunguna da aka amince dasu a fadi...
30/07/2026

Burinmu shi ne SAFMA NATURAL HERBAL CARE ta zama babbar cibiyar samar da ingantattun magunguna da aka amince dasu a fadin Najeriya da ma duniya baki ɗaya, In Sha Allah zamu kasance cikin kawo muku kaya masu inganci da amfani, kamar su zuma zamzam da dukkanin herbal seeds and oi, Muna roƙon Allah Ya albarkaci wannan tafiya, Yasa Albarka da cigaba mai ɗorewa, Allah ya ƙara mana daraja,amana, da yalwar arziki.Ameeeeen.

SAFMA Natural Herbal Care

Loading..... In Sha Allah
27/07/2026

Loading..... In Sha Allah

27/07/2026

من لا حلم له لا مستقبل له 👌

GA DAMA TA SAMU KU GARZAYAALMIHRAB INSTITUTE FOR HERBAL AND PROPHETIC MEDICINE
15/07/2026

GA DAMA TA SAMU KU GARZAYA

ALMIHRAB INSTITUTE FOR HERBAL AND PROPHETIC MEDICINE

Maganin ciwon haƙora (Molars)🦷 _⸙ Kayan haɗi:_ 🥄 Karamin cokali 1 na garin citta.🥄 Karamin cokali 1 na garin kanumfari (...
07/07/2026

Maganin ciwon haƙora (Molars)🦷

_⸙ Kayan haɗi:_

🥄 Karamin cokali 1 na garin citta.

🥄 Karamin cokali 1 na garin kanumfari (clove).

🧄 Tafarnuwa guda 3 a daka su sosai.

_⸙ Yadda ake haɗawa:_

A haɗa dukkan kayan haɗin tare a cikin tukunya mai tsafta. 🥣

A tafasa su da kofi biyu na ruwa tsaftatacce. 💦

Bayan ya tafasa, a zuba ruwan a cikin tukunya ko kwalba mai murfi. 🫙

Sai a zuba wannan haɗin da aka tanada a ciki, a rufe, a bar shi har zuwa safe.

_Yadda ake amfani da shi:_

Ana kurkura wannan ruwan sau biyu a rana.

Za'a samu waraka da yardar Allah.

✍️✍️✍️
SAFMA HERBAL MEDICINE CENTRE*

PHONE/WHATSAPP NUMBER 📱07061620493/ 09078061760

Kuyi following namu domin samun bayani akan cututtuka da maganin su da yardar Allah.

👇👇👇

https://www.facebook.com/profile.php?id=61573819026265

Address

No. 5 Rahama Road Hayin Dan Mani Kaduna
Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SAFMA Natural Herbal Care posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share