ADADE ANAYI HERBAL MEDICINE

ADADE ANAYI HERBAL MEDICINE Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from ADADE ANAYI HERBAL MEDICINE, Medical and health, No:3 Hamisu Abba Plaza opposite karamci clinic bachirawa, Kano.

Lafiya Itace Baban jari ADADE ANAYI HERBAL MEDICINE Muna Bada ingattattun magungunan gargajiya cikin amana da kwarewa da Tsoran Allah Domin Taimakawa Al’umma Wajan Samun Lafiya Da Walwala

18/08/2026
07/08/2026

Anty infection me kyau 07048444430

07/08/2026

Maganin ULSER ME KYAU

07048444430

30/07/2026

DAGA CIBIYAR ADADE ANAYI HERBAL MEDICINE

ADADE ANAYI HERBAL MEDICINE
30/06/2026

ADADE ANAYI HERBAL MEDICINE

30/06/2026

MENENE AMFANIN NAMIJIN GORO A,  JIKIN DAN ADAM ?Namijin goro (wanda ake kira bitter kola a Turanci) wasu ‘ya’yan bishiya...
29/06/2026

MENENE AMFANIN NAMIJIN GORO A, JIKIN DAN ADAM ?

Namijin goro (wanda ake kira bitter kola a Turanci)
wasu ‘ya’yan bishiya ce ta gargajiya da mutane da yawa ke amfani da ita saboda amfaninta ga lafiya. Ga wasu daga cikin muhimman amfaninsa a jikin ɗan adam:

1. 🌿🌿 KARIN KARFI DA KUZARI🌿

Namijin goro na taimakawa wajen ƙara kuzari a jiki, yana sa mutum ya ji ƙarfi da (energy), musamman idan an ci shi da safe.

2. 💝💝 YANA TAIMAKAWA LAFIYAR ZUCIYA💗💗

Yana da sinadarai da ke taimakawa jini (BP) da kuma inganta zagayawar jini, wanda hakan yana taimaka wa zuciya aiki yadda ya kamata.

3. 🫁🫁 YANA TAIMAKAWA HUHU WAJEN NUMFASHI🫁🫁

bincike sun nuna yana taimakawa wajen buɗe hanyoyin numfashi, yana iya taimakawa masu tari ko mura, huhu yayi aiki yanda ya kamata.

4.🍜🍜TAIMAKAWA WAJEN NARKAR DA ABINCHI🍝🍝

Namijin goro na taimakawa ciki wajen narkar da abinci, yana kuma rage matsalar kumburin ciki da rashin jin daɗi bayan cin abinci.

🧠🧠 YANA TAIMAKAWA KWAKWALWA🧠🧠
Yana iya taimaka wa kwakwalwa wajen kasancewa a fresh da lura (alertness), saboda yana da ɗan sinadarin stimulant.

💪💪. YANA QARA LAFIYAR JIMA,I 💪💪

Yana taimakawa wajen qara qarfin sha,awa da samun gamsuwa wajen jima,i.

🚯❌ DA YA KAMATA AKIYAYE❌❌
Ga masu matsalar hawan jini kada su ci da yawa. Domin yana iya kawo matsala kamar bugun zuciya da sauri, hana barchi, da sauransu.

DOMIN KARIN BAYANI ANA IYA TUNTUBARMU TA CIBIYAR Adade Anayi Islam Traditional KO TA NUMBER WAYA KAMAR HAKA 07048444430.07068222777

CIKAKKEN BAYANI AKAN TUMATIRI (Tomato)Tumatiri (Solanum lycopersicum) wata shuka ce daga dangin Solanaceae wacce ake amf...
29/06/2026

CIKAKKEN BAYANI AKAN TUMATIRI (Tomato)

Tumatiri (Solanum lycopersicum) wata shuka ce daga dangin Solanaceae wacce ake amfani da ita a fannoni daban-daban kamar abinci da magunguna. Ana nomanta a sassa daban-daban na duniya saboda wadataccen amfani da take da shi.

ABUBUWAN GINA JIKI DA KE CIKIN TUMATIRI

Tumatiri yana dauke da sinadarai masu amfani ga jiki kamar:

Vitamins:

Vitamin C – yana taimakawa wajen karfafa garkuwar jiki.

Vitamin A – yana da amfani wajen inganta lafiyar ido da fata.

Vitamin K – yana taimakawa wajen haduwar jini.

Minerals:

Potassium – yana taimakawa wajen daidaita matsa lambar jini.

Folate – yana da matukar muhimmanci ga masu juna biyu don ci gaban jariri.

Antioxidants:

Lycopene – wani sinadari ne da ke ba tumatiri ja, yana taimakawa wajen kare jiki daga cututtuka kamar ciwon daji da cututtukan zuciya.

AMFANIN TUMATIRI GA LAFIYA

1. INGANTA LAFIYAR ZUCIYA

Lycopene da Potassium suna taimakawa wajen rage hadarin samun hawan jini da cututtukan zuciya.

2. KARE JIKI DAGA CIWON DAJI

Yawan cin tumatiri yana rage hadarin kamuwa da nau’o’in ciwon daji kamar na mahaifa, nono, fata, da huhu.

3. KYAUTATA LAFIYAR IDO

Vitamin A da lutein da ke cikin tumatiri suna taimakawa wajen kare ido daga ciwon ido da rage hadarin makanta.

4. INGANTA NARKEWAR ABINCI

Yana dauke da fiber da ruwa masu taimakawa wajen hana matsalar hanji kamar ƙwanƙwashewar ciki (constipation).

5. KYAUTATA LAFIYAR FATA

Sinadaran antioxidants da ke cikin tumatiri suna taimakawa wajen hana tsufan fata da rage bayyanar tabo da kuraje.

6. RAGE NAUYIN JIKI

Saboda yawan ruwan da ke cikin sa da karancin kalori, tumatiri yana taimakawa wajen rage kiba.

YADDA AKE AMFANI DA TUMATIRI

1. A ABINCI

Ana amfani da shi wajen dafa miya, tuwon miya, da shinkafa jollof.

Ana hada shi da salati ko sandwiches don karin dandano da sinadaran gina jiki.

Ana iya shan ruwan tumatiri mai sanyi don lafiya.

2. A MAGUNGUNA

Ana amfani da shi a wasu magunguna na zamani saboda sinadaran

Address

No:3 Hamisu Abba Plaza Opposite Karamci Clinic Bachirawa
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ADADE ANAYI HERBAL MEDICINE posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share