31/07/2026
*ALAMOMIN JINNUL ASHIQ A JIKIN MACE (WANDA MAFI YAWAN MATA SUKE DA SHI)*
Kamar yadda kuka sani, *Jinnul Ashiq* wani rukunin wasu shaidanun aljanu ne masu auren mata ba tare da izini ba. Sau da yawa idan ka gan su a jikin mace, ba alkhairi ne ya kawo su ba – musamman idan ita matar aure ce – hakan yana jawo matsaloli a rayuwar aurenta da lafiyarta.
*GA ALAMOMINSA:*
*(1)* Yana saka mace cikin yawan bacin rai. Zakiji zuciyarki tana baci ba tare da wani dalili ba.
*(2)* Haka kuma, ana iya yin mafarki da shi – kodayake ba kowane lokaci ba. Wannan yana danganta da irin ƙarfinsa a jikin mace. Idan ya yi ƙarfi, yana iya sa mace ta ganta tana yin ɗoro daga gaba, ko ta ɗan rankwafa ta baya.
*(3)* Zakiga idan namiji ya zo wajenki, kuna hira lafiya lau, sai kawai ki fara jin nauyin bacci, ko kuma shiru ya k**a ku duka babu abin fada. Soyayya za ta kasance amma babu jin daɗinta ko nishaɗi a zuciya.
*(4)* Shi ba ya hana saurayi zuwa gurinki, amma idan ana shirin yin dariya ko nishaɗi, sai ya tarwatsa zaman. Lokacin da saurayi ya zo gurinki, ku fara hira lafiya, sai ya fara ganin k**ar kin dame shi, ko kin canja masa fuska. Sai ya fara jin cewa *“me ya sa nake son wannan?”* Har ya fara ganin k**ar ya fi ki. Zaki ga yana sauya fuska yana ɓacin rai ba tare da dalili ba. Ke ma hakan na iya shafa ki. Fushi sai ya taso tsakaninku, ku yi faɗa, ku rabu cikin fushi. Amma bayan ya koma gida, zai dawo cikin hayyacinsa, ku rasa yadda abin ya faru. Haka za ku ci gaba, har a zo batun aure, amma sai kawai soyayyar ta mutu, kuma ba za ki sake jin shi ko ganinsa ba – ku rabu kenan.
*(5)* Ko kuwa idan za a yi magana da namiji kan aure ko a turo gida, sai kawai a rasa shi. Ko idan aka yi maganar aure, sai ya ki dawowa ko ya canja shawara.
*(6)* Ga matan aure kuma, yana hana haihuwa. Ko idan an samu ciki, sai ciki ya zube. Ko kuma babu dalili, ta rika faɗa da mijinta. Zata dinga fushi da kan abu mai sauƙi.
*(7)* Mace za ta iya yawan mafarkin namiji yana saduwa da ita.
Maganinsa yana da wahala, domin ko an yi magani sau da yawa ba ya warkewa gaba ɗaya. Sai dai a samu sauƙi, domin wani lokacin maganin kan ɓata maimakon warkarwa.
*Wannan kadan ne daga cikin alamomin Jinnul Ashiq a jikin mace. Allah Ya karemu daga sharrinsu, Ya ba mu kariya. Ameen.*
Domin haɗin maganin ka a tuntuɓemu ta Whatsapp/Kira
08131861171
09041529292
✍️✍️✍️C.E.O Al-AFWAH HERBAL MEDICINE LTD