Kiwon Lafiya A Matakin Farko

Kiwon Lafiya A Matakin Farko Lafiya uwar jiki babu mai fushi da ke !

04/06/2024

Insha Allahu za muyi bayani daya bayan daya na Ka'idojin Kiwon Lafiya A Matakin Farko nan gaba.

A cigaba da bibiyar mu!

04/06/2024

Ka'idojin Kiwon Lafiya A Matakin Farko

Sune ;

*Hallarar Jama'a Cikin Sha'anin Kiwon Lafiya

*Hadin Gwiwa Da Sauran Kungiyoyi

*Yin Amfani Da Fasahar Data Dace

*Daidaita Rabon Kula Da Lafiya

*Inganta Jami'an Kiwon Lafiya

04/06/2024

Manufofin Kiwon Lafiya A Matakin Farko

Sune ;

*Domin habbaka shiga aikace-aikacen kula da lafiya

*Domin habbaka nagartacciyar kula da lafiya

*Domin habbaka yawan masu lafiya

04/06/2024

Mece Kiwon Lafiya A Matakin Farko (Primary Health Care) ?

Itace muhimmiyar lafiya wadda ake gwadata a kimiyance, cikin karbabbiyar walwala da fasaha, wadda aka mayar da ita yadda kowa zai iya samunta a ko ina cikin duniya daga mutum daya har iyali acikin al'umma tare da cikyakken hadin kansu a yanayin da al'umma da kasa baki daya zasu iya samu a saukake, acikin ruhin dogaro dakai da azamar kashin kai. (Sanarwar Alma Ata, a shekarar 1978)

Kiwon Lafiya A Matakin Farko ya kunshi abubuwa kamar haka;

Manufofi (Objectives)
Ka'idoji (Principles)
Bangarori (Components)

03/06/2024

Lafiya

Me cece lafiya ?

Lafiya itace zama da cikyakken jiki da hankali, da walwala, bawai rashin cuta ba.

03/06/2024

Assaalamu Alaikum

Yan'uwana maza da mata wa yanda suke jin yaren hausa !

Wannan fejin mai suna " Kiwon Lafiya A Matakin Farko" an kirkire shi domin kiwon Lafiya a matakin farko da wayar da kai, iyali da sauran al'umma baki daya.

Zai dinga zuwa muku da matakai na kariya da kula da lafiya a matakin farko.

Zai kuma bada dama wajen tambayoyi ga masu biye da fejin da amsa musu tambayoyin su.

Mun gode,

Lafiyar Jama'a ita ce damuwar mu !

Address

Zakirai
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kiwon Lafiya A Matakin Farko posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share