30/08/2025
SIRRUKAN BISHIYAR GUAVA (Maganin Gargajiya)
بسم الله الرحمن الرحيم
Allah Bai Halicci Wata Bishiya ko ganye a banza ba, kowane bishiya da ya halitta tana da irin sirrukan ta da magunguna da take yi a jiki dda ruhin ɗan Adam.
A yau zamu yi magana akan Bishiyar Guava da amfaninta a magungunan gargajiya:
GANYEN GUAVA:
Ana Tafasa Ganyen Guava A Ruwa, A Sha Shi Kamar Shayi.
Yana Maganin:
1. Zawo (diarrhea)
2. Ciwon Ciki Da Kumburin Ciki
3. Matsalar Narkewar Abinci (indigestion)
Kuma Ana Kurkure Baki Ko Wanke Baki Da Ruwan Ganyen Guava Wanda Aka Tafasa, Yana Maganin Warin Baki Yana Kuma Ƙarfafa Dadashi.
ƳAƳAN GUAVA (Guava Fruit):
1. Cin Ƴaƴan Itaciyar Guava Yana Ƙara Ƙarfin Garkuwar Jiki.
2. Cin Ƴaƴan Itaciyar Guava Yana Taimakawa Wajen Saukar Da Sugar Ko Rage Sugar Da Yake A Cikin Jini (blood sugar) Ga Masu Ciwon Sukari.
3. Cin Ƴaƴan Itaciyar Guava Yana Ƙara Lafiyar Ido Da Fata.
SIRRIN MAGANIN TSORO DA TASHIN HANKALI KO RUƊANI:
Idan Aka Sami Ganyen Guava Sai Ayi Shayi Dashi. Sai A Karanta Ayatul Kursiyyu Kafa 7 A Tofa A Ciki A sha. Yana Magani Na Kariya Daga Tsoro Da Ruɗani (anxiety).
A Jarraba Za A Godewa Ni'imar Allah Kuma Za A Riski Albarkar Da Take Acikin Wannan Bishiya. Ayi Mana Like Da Share Domin Al'ummar Annabi (S.A.W.A) Su Amfana.
“Allah Bai Halicci Wata Cuta Ba Sai Da Ya Halicci Maganinta.”
اللّهُمَّ اجعل في هذا الدواء نوراً وشفاءً وبركة، واحفظنا ببركة محمد وآل محمد