29/08/2026
Ba ko da yaushe ba ne idan malami ya yi magana a kan wata mas'ala yake nufin ya karɓi kwangila ko kuma an saye shi da kuɗi.
Sau da yawa, iyakar gaskiyar da yake faɗa ce, da kuma fahimtarsa game da rayuwa gwargwadon ilimi da ikon da Allah Ya ba shi.
Don haka, idan ya faɗi ra'ayin da ya saba da naka, kai ma kana iya bayyana naka ra'ayin ba tare da zagi ko cin mutunci ba.
Ka tuna, shi ma mutum ne, kuma mutum yana iya yin kuskure wajen fahimta ko aiki. Babu wani mutum da aka ba kariya daga yin kuskure.
Saboda haka, mu riƙa duba alheran da ke tattare da mutum, sannan mu yi ƙoƙarin kau da kai daga kurakurensa.
Allah Ya gafarta mana baki ɗaya, Ya shiryar da mu zuwa ga gaskiya, Ya kuma sa mu zama masu adalci wajen mu'amala da juna. Ameen.