Dr Ridwan Ibrahim wanzam and son's herbal medicine center

  • Home
  • Dr Ridwan Ibrahim wanzam and son's herbal medicine center

Dr Ridwan Ibrahim wanzam and son's herbal medicine center Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dr Ridwan Ibrahim wanzam and son's herbal medicine center, Medical and health, Jaji Road Tudun wada kasuwa barchi kaduna, .

16/10/2023

MAGANIN KOWACCE IRIN ULCER SAI DAI IN TA AJALI CE...

Ƙaƙƙarfan maganin ulcer wanda duk mai ita in ya sha ya warke wallahi sai dai in ciwon ajaline don ciwon ajali ba shi da magani to ga maganin:-

1* GARIN GANYEN ZOGALE
2* GARIN GANYEN BADO
3* NONO KO MADARA

A haɗa garin zogale da na bado guri daya a juya shi ya juyu to kullum mai ulcers in zai kwanta barcin dare sai a samu nono ko madara sai a yi cokali biyu na garin maganin a sa nonon a juya a sha kwana bakwai an warke da yardar Allahu.

16/10/2023

BAYANI AKAN CIWON KANSA NA NONO (BREAST CANCER) ALAMOMIN TA DA MAGANIN TA FISABILILLAH.

DON ANNABIN RAHMA IDAN KA KARANTA KA TURA DOMIN SAURAN UWA SU AMFANA.

Ciwon daji na Nono (breast cancer) yana faruwa ne lokacin da wani sauyi da ake kira maye gurbi (mutations)ya faru a cikin kwayoyin halittar da ke daidaita girman kwayar halitta.

Maye gurbi (mutations) yana barin kwayoyi(cell) su rarrabuwa kuma su ninka ta hanya mara sarrafuwa.

Cancer ta nono kansa ce da ke faruwa a cikin ƙwayoyin nono,yawanci ciwon daji yana samuwa a cikin lobules ko ducts na nono.

Lobules sune gland(bututu) dake samar da ruwan Nono, ducts kuma sune hanyoyin dake kawo madara daga gland(bututu) zuwa bakin nono. Ciwon daji kuma na iya faruwa a cikin nama mai kitse ko nama a cikin nono.

A farkon matakin ciwon nono bazai haifar da wata alama ba yawancin lokuta, ciwace-ciwacen daji na iya zama ƙanana da ba zaa iya ji ba, amma har yanzu ana iya ganin rashin daidaituwa akan mammogram (magwajin cutar)

Idan ana iya jin kumburi, alamar farko yawanci sabon kululu ne a cikin Nono da babu shi a can baya,duk da haka ba kowanne kululu bane yake nufin akwai ciwon daji na nono

Kowane kalar ciwon daji na nono yana iya haifar da alamu iri-iri,yawancin waɗannan alamun suna k**a da juna, amma wasu na iya bambanta.

Alamomin cutar sankarar nono da aka fi sani sun haɗa da::

1. Fatar nono tayi ja,sannan Nonon ya rika yin zafi idan aka taba shi ko haka kawai.
2. Jin radadi a cikin Nonon
3. Fitar jini daga kan Nono.
5. Fitar ruwa k**ar Nono wanda kuma shi ba Nono bane
6. Kumburi ko jin zafi a kasan hannu.
7. Ganin sauyi a kalar fatar Nono.

Ganin wani daga cikin alamomin nan ba shine zai iya tabbatar da kina dauke da cancer Nono ba,misali jin zafi a Nono yakan faru lokacin da wani kurji zai fito a wajen wanda ba cancer ba.

Rabe-Raben Ciwon Cancer Nono.

1. Triple-negative breast cancer
2. Metastatic breast cancer
3. Inflammatory breast cancer.

Sannan cutar cancer tana da matakai har guda hudu.

Address

Jaji Road Tudun Wada Kasuwa Barchi Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr Ridwan Ibrahim wanzam and son's herbal medicine center posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Health & Beauty Business?

Share