24/02/2026
Yadda zaka kauce warin baki
1. Goge baki da kyau
Wanke baki sau 2 a rana (safe da dare).
Kada ka manta da goge harshe, domin datti yana taruwa a kai sosai.
2. Amfani da ruwan gishiri
Ka zuba rabin cokali na gishiri a cikin kofi 1 na ruwan ɗumi.
Ka kurkura baki da shi sau 1–2 a rana.
3. Shan ruwa sosai
Ruwa yana taimakawa wajen hana baki bushewa.
Idan baki ya bushe, warin yana ƙaruwa.
4. Tauna citta ko mint
Ƙaramin yanki na citta ko ganyen mint yana rage wari.
Hakanan zaka iya amfani da chewing gum mara sukari.
5. Kauce wa taba da yawan albasa/tafarnuwa
Wadannan suna ƙara warin baki.
6. Duba hakori
Idan warin bai daina ba bayan ka gwada waɗannan, yana da kyau ka je asibitin hakori domin a duba ko akwai ciwon cingam ko ramuka.