Nihmat herbal medicine and therapies centre

Directions

Nihmat herbal medicine and therapies centre Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Nihmat herbal medicine and therapies centre, Medical and health, Masamawa primary school, Birnin-Kudu.

AlhamdulillahNIHMAT Herbal Medicine & Therapies ya fara aikiMuna bayar da shawara da magungunan gargajiya bisa ilimi
01/02/2026

Alhamdulillah
NIHMAT Herbal Medicine & Therapies ya fara aiki
Muna bayar da shawara da magungunan gargajiya bisa ilimi

DORAWA ITACE MAI ALBARKA 1-GANYEN DORAWA 2-SASSAQE DORAWA 3-KAUCE DORWA4-SAIWA DORAWA 5+FURE DORAWA (TUNTU)'6-YA'YA DORA...
05/04/2025

DORAWA ITACE MAI ALBARKA

1-GANYEN DORAWA
2-SASSAQE DORAWA
3-KAUCE DORWA
4-SAIWA DORAWA
5+FURE DORAWA (TUNTU)
'6-YA'YA DORAWA (KALWA)
7-GARIN 'YA'YA (GARIN DORAWA)
8'-YA'YA DORAWA (MAKUBA)

KO WANNE A CIKIN SU MAGANI NE NA MUSAMMAN A GARGAJIYANCE

GANYEN DOROWA
1-ASMA
Shan Garin Ganyen Dorawa Rabin Cokali a Ruwan Dumi Yana Maganin Asma
2-CUTAR FATA
Ana Dafa Danyen Ganyen Dorawa Ayi Wanka Dashi Ruwan Da Dumi Yana Maganin Cututtukan Fata

SASSAKEN DORAWA
1-SAURIN JIN FITSARI
Wanda ke Fama da Yawan Yin Fitsari Akai-Akai,
Ya Nemi Sassaken Dorawa Ya Dafa Yana Sha Zai Rabu da Wannan Matsalar
2-ZAFIN CIKI
Wanda Cikin Shi Ke Yawan Daukar Zafi Ko da Yaushe Yasha Garin Sassaqen Dorawa Sau Daya Arana Kwana 3

SAIWAR DORAWA
1-SANYI
Ana Dafa Saiwar Dorawa da Jar Kanwa Asha Sau Daya Kwana 3 Tana Maganin Sanyi
2- KURGA
Ana Dafa Saiwar Dorawa Idan Ta Huce Ya Koma Mai Dumi A Tsuma Yaro Yana Maganin Kurga

BOWON DORAWA
1-TARI
A Dafa Bawon Dorawa Guda Daya Rak da Ruwa Lita 2 Asha Qaramin Kofi Sau daya a rana Lokacin da zaa Sha Asa Zuma Cokali Daya a Sha Kofi Daya Kullun Har Ya kare Cikin Ikon Allah Ko Wanne Irin Tari ne Zaa Rabu da shi
2-BASIR
Garin Bawon Dorawa Mai Laushi Asha Cokalin Nescafe Sau Daya A Rana a Kowanne Irin Nuin abin Sha Zaa Rabu da BASIR Ko Wanne Irin ne

'YA'YAAN DORAWA (KALWA)
1-KANSA
Garin Yayan Dorawa na Maganin Kansa ko Wacce Iri Idan Ana Shan Shi da Nono
2-MAKOKO
A Soya Yayan Dorawa A Maida Su Gari Ana Sha A Ruwan Dumi Maganin Makoko ne

KAUCEN DORAWA
1-TAIFOT
A Dafa Kaucen Dorawa A Sha karamin Kofi Sau Daya ARana Yana Maganin Taifot Komai yawan shi Ajiki
2-CIWON GABOBI
Mai Fama da Ciwon Gabobi Ya Dafa Kaucen Dorawa Yasha Zai Sami Lafiya

FUREN DORAWA
1-CIWON KODA
A Dafa Furen Dorawa A Sha karamin Kofi na Ruwan Mako 3 Yana Maganin Ciwon koda
2- KUMBURI -KO AMAI
A Maida Furen Dorawa Gari Asha karamin Cokali a Kowanne Irin Abin Sha Sau 2 A Rana Kwana 7 Duk yadda Matsalar Kumburi ta Kai Zaa Sami Lafiya In Sha'Allahu

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu!Ina taya ku murna da zagayowar wannan rana mai albarka. Allah ya karɓi ib...
02/04/2025

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu!
Ina taya ku murna da zagayowar wannan rana mai albarka. Allah ya karɓi ibadunmu, ya gafarta mana kura-kuranmu, ya kuma cika mana dukkan bukatunmu na alheri.
Allah ya sa mu rayu cikin lafiya, albarka, da zaman lafiya. Mu ci gaba da jin daɗin rahamarSa a duniya da lahira.
Eid Mubarak!

ANFANIN SHAN SHAYIN TAZARGADE DA KANINFARI.Ka daure kayi share domin Al'umma su amfana.Shekaru da dama ana amfani da Taz...
14/02/2025

ANFANIN SHAN SHAYIN TAZARGADE DA KANINFARI.

Ka daure kayi share domin Al'umma su amfana.

Shekaru da dama ana amfani da Tazargade wajen magance manyan cutukan da suke damun Al'umma saboda tana da sindarai wadan da suke kace cutuka da dama a jikin mutum cikin kankanin lokaci.

Kadan daga amfanin shayin Tazargade da kaninfari.

1. Magance ciwon kai.
2. Magance zazzabin maleria.
3. Magance bacin ciki.
4. Magance zafin zuciya.
5. Magance infection.
6. Magance raunin mazakuta.
7. Karfafa garkuwar jiki.

Da sauran su.

Yadda za'a hada shayin shine:

Zaka samo garin Tazargade teaspoon daya kaninfari rabin teaspoon a hade da ruwa kofi 2 a dafa,zaa iya saka sukari kadan ko zuma a ciki.

A rana 2 a sha kofi 1 safe 1 yamma kamar kwana 7 insha Allah.

WALLAHU A'ALAM.

Masu fama da Larurar tarin fuka wato TUBERCULOSIS dake samun magunguna kyauta suma wannan janye tallafin ya shafesu baya...
31/01/2025

Masu fama da Larurar tarin fuka wato TUBERCULOSIS dake samun magunguna kyauta suma wannan janye tallafin ya shafesu baya ga masu HIV

Hakazalika dukkan wani tallafi dake zuwa da US domin yaqi da cutar Malaria shima an tsaida shi.

Kai Bama wannan ba, duk wani NGO Project da tallafinsa ke fitowa daga Amurka an dakatar dasu. Haka ɓangaren tallafi ga jarirai, wanda yana iya kasancewa har al'amarin allurar riga-kafi da akewa yara shima ya zamo zuwa gaba sai an saya.

Shugaban ƙasar ya bayyana zai sami wata uku yana nazari kan dakatarwar amma fa kwai yiwuwar tallafin ya tafi kenan.

A nan nake qara jawo hankalinku da ku qara kula da lafiyarku kunsan de abinda Amurka ta nuna kashe kudade yayi yawa bazata iya ba shugabannin ƙasar mu dama ba'a ma zancen su... Naji wani babban kamfanin Magani shima ya fara tattare kayansa daga Nigeria, dama wasu tuni sun tafi.

Toh Allah ya cigaba da tsare mu, amma muna cikin damuwa, domin ɗaya daga illar shine mutanen mu sun ƙware wajen ha'inci da yin magani marasa inganci.... Kaita sha ba canji, idan aka barmu dasu suma kaɗai sun ishe mu, ballantana kuma wadancan cuttukan dake iya yaɗuwa.

SUNAYEN WASU MAGUNGUNA DA AKE AMFANI DA SU DOMIN MAGANCE CUTUTTUKACikin harshen Larabci, Hausa da kuma Turanci.Sharaɗin ...
07/01/2025

SUNAYEN WASU MAGUNGUNA DA AKE AMFANI DA SU DOMIN MAGANCE CUTUTTUKA
Cikin harshen Larabci, Hausa da kuma Turanci.

Sharaɗin shine ayi sharing domin yan uwa su amfana 🛎

1. Black Seed- حبة البركة (Habbatus sauda)

2. Honey - عسل (Zuma)

3. Olive Oil - زيت الزيتون (Man Zaytun)

4. Dates - تمر (Dabino)

5. Barley - شعير (Sha'ir)

6. Pomegranate - رمان (Rumman)

7. Fig - تين (Ɓaure)

8. Cucumber - خيار (Gurji)

9. Ginger - زنجبيل (Citta)

10. Garlic - ثوم (Tafarnuwa)

11. Onion - بصل (Albasa)

12. Mint- نعناع (Na'ana'a)

13. Cumin- كمون (Kammun)

14. Fennel - شمر (Shammar)

15. Saffron- زعفران (Za'afaran)

16. Cardamom - هيل (Hayil)

17. Rosewater - ماء الورد (Ma' ul-Wardi)

18. Coriander - كزبرة (Kuzbara)

19. Aloe Vera- صبار (Alobera)

20. Pepper - فلفل (Barkono)

21. Turmeric- كركم (Kurkur)

22. Mustard - خردل (Khardal)

23. Anise - يانسون (Yansun)

24. Sesame Seeds - سمسم (Kantu/Riɗi)
25. Basil- ريحان (Ɗoɗɗoya)

26. Thyme - زعتر (Si'itir)

27. Licorice - عرقسوس (Irƙusus)

28. Sage - مريمية (Miryamiyyah)

29. Grapes- عنب (Inibi)

30. Coriander- كزبرة (Kuzbara)

Idan kuna bukatar sanin amfanin wani itace ko wani sinadari ko yadda ake haɗa maganin wata cuta sai ku rubuta mana a comment, za mu kawo muku, insha Allahu.

Address

Masamawa Primary School
Birnin-Kudu

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nihmat herbal medicine and therapies centre posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share