Charity Foundation Dutsin-Ma

Charity Foundation Dutsin-Ma To serve and assist A humanitarian organisation that helps orphans and poor ones.

ZIYARAR CHARITY FOUNDATION DUTSINMA A GIDAN GYARAN HALI NA KARAMAR HUKUMAR DUTSINMA.Gidauniyar Charity Foundation Dutsin...
22/03/2026

ZIYARAR CHARITY FOUNDATION DUTSINMA A GIDAN GYARAN HALI NA KARAMAR HUKUMAR DUTSINMA.

Gidauniyar Charity Foundation Dutsinma ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Malam Tanimu Bala Dutsinma, tare da sauran mambobinta, sun kai ziyara zuwa Gidan Gyaran Hali na Karamar Hukumar Dutsinma domin yin barka da Sallah da kuma ƙarfafa zumunci.

Wannan ziyara da aka kai ranar Lahadi, 22/03/2026, na daga cikin ayyukan alheri da gidauniyar ke yi lokaci bayan lokaci, domin tallafawa da kuma kula da ‘yan’uwa a irin waɗannan wurare.

A yayin ziyarar, an samu halartar ɗaya daga cikin manyan malaman karamar hukumar Dutsinma, Malam Kabir Abdullahi Yalwa, wanda ya gabatar da nasiha mai muhimmanci ga mazauna gidan, tare da ƙarfafa musu gwiwa kan gyaran hali da komawa tafarki madaidaici.

A ƙarshe, Gidauniyar ta isar da saƙon ta na tausayi, ƙauna da kuma fatan alheri ga waɗannan bayin Allah, tare da basu gudummawar da za ta taimaka musu wajen gudanar da bukukuwan Sallah cikin sauƙi.

ADDU’A:
Muna roƙon Allah (SWT) Ya karɓi wannan aiki na alheri, Ya saka da mafificin alheri ga Gidauniyar Charity Foundation Dutsinma da dukkan waɗanda s**a taimaka wajen ganin an gudanar da wannan ziyara.

Allah Ya taimaki mazauna wannan gida, Ya sauƙaƙa musu halin da suke ciki, Ya shiryar da su zuwa hanya madaidaiciya, Ya kuma basu damar fita su zama ‘yan ƙasa nagari masu amfani ga al’umma.

Allah Ya ƙara haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Dutsinma baki ɗaya, Ya kuma sa mu kasance masu taimakon juna da tausayi a dukkan al’amuranmu.

Amin.

Ofishin Hulɗa da Jama’a
CFD.

22/03/2026

Ziyarar Charity Foundation Dutsinma a Gidan gyaran hali na Dutsinma

21/03/2026

TUNATARWA
Gobe lahadi karfe 9am ziyara gidan gyaran hali( gidan yari). A zo da wuri domin a gama da wuri. Allah ya kaimu Amin

Charity Foundation Dutsinma zata yi bikin karamar Sallah tare da yanuwa musulmi da ke a gidan gyaran hali da ke a Dutsin...
19/03/2026

Charity Foundation Dutsinma zata yi bikin karamar Sallah tare da yanuwa musulmi da ke a gidan gyaran hali da ke a Dutsinma.

Kamar yadda ta saba a duk bikin sallah, Gidauniyar tana kai ziyarar domin taya yanuwa da Allah ya jarabta da kasancewa a gidan gyaran hali murna tare gabatar musu da abincin Sallah da kuma wasu kayan buƙata. A wurin walimar ana gabatar da takaitacciyar NASIHA tare da sauraron masu karamin laifuka musamman BASHI domin shiga cikin alamarin domin a samu mafita.

Akan haka ne Charity Foundation Dutsinma take kira ga masu hali da su taimaka ma wannan aiki da duk abunda Allah ya h**e.

Za'a iya tuntubar Shugaban ƙungiyar Tanimu Bala 0806 832 1750 ko shugaban Kwamitin zuwa gidan gyaran halin watau Kabir Ahmed 0806 387 5670 Allah ya bada ikon taimakawa Amin

Za'a yi wannan walima a ranar Lahadi 22/3/2026 da karfe 9am Allah ya bada ikon zuwa Amin

15/03/2026
15/03/2026

Kai tsaye wurin gabatar da ɗunkunan sallah ga marayu daga gidauniyar Charity Foundation Dutsinma.

14/03/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! مختار ثسكي, Besty Adam, Saraki Mai-Allah

14/03/2026

Happy follow-versary to my awesome followers. Thanks for all of your support! Halimatu Tafokee

Address

No. 2, Kankia Bye-Pass/Opp. Dutsin-ma Motors
Dutsin-Ma

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Charity Foundation Dutsin-Ma posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Charity Foundation Dutsin-Ma:

Share