30/05/2026
AL-ISHRAH MARRIAGE AND FAMILY COUNSELING CENTRE FUNTUA.
Ta kai ziyarar gaisuwar Sallah ga wasu daga cikin iyayen ta
A Ranar Juma'a 29-05-2026 kwana biyu da Babbar Sallah, wannan cibiya mai albarka ta ziyarci wasu daga iyayen ta, domin gaisuwar sallah tare da neman karin shawarwari daga gare su.
Wadanda muka samu damar ziyarta sun hada da
1. Mai Girma Magajin Garin Funtua
Alh. Shehu Nuhu
2. Sheik Umar Shuaibu Funtua
Mataimakin Shugaban JIBWIS FUNTUA
3. Sarkin SAMARIN FUNTUA (I)
Alh. Faruk Ibrahim
4. Dr. Aminu Isah Musa Funtua
Shugaban Kwamitin Matasa JIBWIS Funtua
Da dai sauran su.
A lokacin ziyarar mun samu muhimman shawarwari daga garesu tare da karfafa gwuiwa akan ayyukan da Cibiyar AL-ISHRAH ta ke Gabatarwa.
✍️
Nasiru Sulaiman Funtua
P.R.O AL-ISHRAH