29/03/2026
TARIHIN RUWAN ZAMZAM DA KUMA FA'IDAR SHAN RUWAN ZAMZAM
Daga shafin Bashir Halilu
Annabi Ibrahim عليه السلام
ya zauna tare da matarsa Saratu عليها السلام
a Kasar Falasdinu tsawon lokaci amma ba su samu haihuwa ba.
Ita kuma tana fatan Allah Ya baiwa Annabi Ibrahim عليه السلام wanda zai gaje shi.
Don haka sai ta ba shi Baiwarta mai suna Hajara عليها السلام
ya aura.
Sai Hajara عليها السلام
ta haifar masa da mai suna Isma'ila عليه السلام.
Don haka Sai Annabi Ibrahim عليه السلام
da matarsa Saratu عليها السلام
s**ay farin ciki sosai da samun wannan da.
Sai Allah Madaukakin Sarki Ya umarci Annabi Ibrahim
عليه السلام
ya dauki matarsa Hajara da jaririnta Ismail ya kaisu inda garin Makka yake a yanzu.
Sai Annabi Ibrahim ya bi umarnin Allah Madaukakin Sarki ya cewa matarsa ta zo ta raka shi unguwa.
Sai ta dauko jaririn nata ta goya shi, ta bi Annabi Ibrahim عليه السلام
s**a cigaba da tafiya. Ba ta san inda za a je ba amma saboda biyayya tana biye da shi.
Har saida s**a iso daidai garin Makka. A lokacin babu gini ko daya a wajen. Ba mutane, ba bishiyoyi, ba ruwa, ba abinci, ba tsuntsu, ba wata dabba, ba komai a wajen sai Sahara da duwatsu.
Sai Annabi Ibrahim عليه السلام
yay mata umarni ta zauna a wajen.
Sai ta zauna. Shi kuma ya juya yay tafiyarsa.
Sai ta kwalla masa kira ta ce " Ya Annabin Allah!, ka kawo mu nan wajen, ba abinci ba ruwa ba kowa a wajen kuma ka juya ka tafi ka bar mu".
Sai Annabi Ibrahim عليه السلام
ya tasaya, ba tare da ya juyo ya kalleta ba kuma bai ce mata komai ba.
Sai ta sake ce masa " Ko Allah ne Ya umarce ka ka kawo mu nan?".
Sai ya ce mata "E".
Sai ta ce masa "To je ka ba komai. Tunda Allah ne Ya sa ka kawo mu na san zai kula da mu".
Sai Annabi Ibrahim عليه السلام
ya tafi ba tare da waiwayo ya kallesu ba, saboda kada tausayinsu ya k**a shi ya kasa zartar da umarnin Allah.
Don haka yay musu addu'a ya wuce abinsa.
Bayan Annabi Ibrahim عليه السلام ya tafi, sai Jaririn Hajara
عليها