14/07/2026
Idan ƙaddarar soyayya ta haɗa ka da ɗiyar talakawa (mai rawar kai), ka yi duk yadda zaka yi ku daidaita tsakanin ku tun a t**i kafin ku yi aure musamman kan abinda ya shafi ƙawaye. Idan ka kuskura ka auri macen da take da ɗanyen kai wadda bata iya banbance Nafila da Farilla, wlh ina maka rantsuwa da Allah sai ka wayi gari kana sha'awar rayuwa da dorunar ruwa fiye da ita am telling you. Idan ka kuskura ka auri yarinyar da duniya ce kawai a gaban ta, wlh har abada ka yi hannun riga da kwanciyar hankali a cikin rayuwar ka ta aure. Kana ji kana gani yarinya zata haɗa maka koko da giya kuma dole ka shanye ba yadda zaka yi wlh.
Idan ka sake ka auri yarinyar da sam bata ɗaukan haske kan abubuwan da s**a zama dole da waɗanda kuma s**a zama na sukuni, na rantse maka da Allah ba ruwan ta da yanayin da zaka shiga ko mutuwa zaka yi saidai ka mutu matuƙar ita ɗin buƙatar ta ta biya. Idan ka haɗu da 'yar yarinya, kana zaune zata ɗauko maka rayuwar da ake yi a gidan ƙawayen ta tace kuma dole irin ta zaku yi koda zaka shiga wahala wannan kuma ruwan ka ne. Kar ka ɗauka don kuna soyayya da yarinya a t**i tana yi maka ɗauki ba daɗi kayi tsammanin idan kun yi aure zata canza. Babu abinda zai canza matuƙar baka taka mata birki ba. Kar ka sake wauta tasa yarinya take wuce maka gona da iri tun a t**i kuma ka ɗauka abun zai wuce bayan kun yi aure. Tun a wata biyun farko zaka gane Allah ɗaya ne baida abokin tarayya.👌