29/08/2026
📑 AMFANIN CIYAWAR NONON KURCIYA 📝
1- TSUTSAR CIKI DA GUDAWA/ATINI: Ana samun ganyenta akirɓa asa ruwa agauraya atace asha ko abusar da ganyen adaka atankaɗe azuba ƙaramin chokali a kunu ko aruwan zafi rabin kofi asha sau biyu arana idan abun yayi yawa asha sau uku.
2- CUTUTTUKAN FATA: Ƙuraje, makero, saɗore, amosani, kora, ƙaiƙayin jiki, kurkunu da sauransu sai asamu ganyenta a jajjaga agoga awajen ko abusar da ganyen adaka atankaɗe akwaɓa garin da man kaɗanya adinga shafawa.
3- RUWAN NONO: Wacce take buƙatan ruwan nono lokacin shayarwa saita busar da ganyen tadaka ta tankaɗe tahaɗa garin da garin hulba tadinga zuba chokali ɗaya a ruwan zafi (asa madara) tasha.
4- SANYIN ƘASHI DA GAƁOƁI: A jajjaga ganyenta a goga a inda yake ciwo koda akwai kumburi zai saɓe sannan ana daka ganyen tareda saiwar a kwaɓa garin da Man shanu ko man kaɗanya a shafa a wajen.
5- CIWON KUNNE: Ana ɗiga farin ruwan dake fita daga Nonon kurciya idan an tsinki ganyen aɗiga ruwan a kunne musamman idan kunnen yana ruwa.
6- ƘURAJEN CIKIN BAKI/MAƘOGORO DA HARSHE DA GYAMBON CIKIN BAKI (MOUTH ULCER):
Ana wanke ganyen Nonon kurciya a tauna a baki a haɗiye ruwan.
7- CIWON KAI: A mutstsuka ganyen agoga a goshi da izinin Allah zai daina ciwo.
8- CIWON ASTHMA, PNEUMONIA, TARI, FITSARIN JINI, JIN ZAFI LOKACIN FITSARI, DAFI, INFECTION, TSUTSAR CIKI:
Ana samun ciyawar Nonon kurciya harda itacen kamar cikin hannu a wanke a zuba ruwa kofi 2 a dafa a tace asha rabin kofi safe da yamma zuwa kwana 3 ko sati 1 sannan za'a iya shanyashi ya bushe a daka yayi laushi a dinga shan chokali 1 a nono ko kunu anasha ko a kwaba da zuma ga masu Asthma ko Pneumonia adinga shan chokali ɗaya.
9- RARIYAR HANNU: Ana daka nonon kurciya dukanta ashanya idan ta bushe asake dakawa sama sama sai adinga tirara hannu dashi.
10- CIWON IDO: ciwon ido kowane irine ko hakiya asamu ganyen a wanke sai asa ruwa a markada ko a jajjaga asa ruwa atace adinga ɗiga ruwan
Ayi share sauran yan uwa su amfana
Call or whatsapp09023624451