07/06/2026
A kaf nazarin da nayi babu wata mujallar likitanci ko ta lafiya data kawo wani sahihin binkice guda ɗaya tak na wata cuta da wani mutum ko wasu al'ummai s**a haɗu da ita har tai ajalinsu dalilin cin biredi.
Illa iyaka kwai gurare uku da Biredi ke iya yin kisa:
1. Ƙwarewa wato choking yayin cin biredi idan yagosa har yafi karfin wucewa ta cikin makogoronka hakan na iya jawo ya toshe bututun iska wanda mutum na iya samun karancin iska wato asphyxia wanda ka iya jawo mutuwa idan har ba adau matakin ciresa ko ƙaƙarosa ba.
Wanda kuma duk sauran abinci na iya wannan kamar su doya, dankali, da sauransu, kai ruwa ma na iya kwareka ka mutu.
2. Idan ya zamto biredin gurbatacce ne wato da gangan ansa wata guba a jiki ko kuma bisa kuskure an ajesa waje mara tsafta da kwayoyin cuta ko wata guba ke iya shiga jikinsa da in anci zai iya lalata jiki, ya haddasa ƙullewar ciki ko gudawa, ko saukar jini wanda shima za'a iya mutuwa.
Wanda kuma kowanne abinci ma na iya kisa ta wannan hanyar inya zamto contaminated.
3. Shine Allergy, wato kwai mutanen da basa cin alkama ko abincin fulawa saboda jikinsu baya so, kamar yadda wasu basa cin gyada saboda jikinsu bayaso, idan s**a ci nan da nan suna iya fuskantar matsalar borin jini, duk jikinsu ya tashi yai rudu-rudu, fuskarsu da idanunsu da bakinsu su kumbura wanda kumburin har makoshinsu wanda hakan kan jawo toshewar butuntun iska wato wind pipe obstruction inda nan ma mutum na iya mutuwa dalilin karancin iska kamadr yadda choking ke kisa.
Don haka me wannan matsalar dama idan ya sani baya cin biredi.
______________________________________
In banda wannan guraren ba abinda ya hada biredi da kisa, na fada zan kuma maimaitawa biredi ba guba bane. Kuma kamar kowanne abinci inde a wannan zamanin namu ne to kowanne ka dauka kace zakai masa ƴar tinke sai ka sami inda yake da tasa irin illar.
Hatsarin biredi ya haddasa ciwon cancer ko kisa dalilin sinadaran cikinsa irinsu potassium bromide ko a wani binkice da akai a jihar EKITI dake Nigeria shine: Mutum 22 cikin milyan ɗaya na manya da kuma mutum 56 cikin milyan guda na yara kanana. A hakan ma bawai ya taba kashewa ko ansami illar bane kurum risk ne.
Toh Kaga ko malaria ma ta ci ubansa illah sama da sau dubu, domin milyoyi take kashewa duk shekara ita.
Matsalar mu shine shagala da abinda bai kaima mu tsaya mu tattaunawa a kansa bama amma sai ya zama topic of discussion
Ibrahim y Yusuf