22/07/2026
MEYASA MUKE AMAI?
Ka taɓa tambayar kanka me yasa muke amai?
Shin cikin mutum ne yake yanke shawarar yin amai, ko kuwa akwai wani sashe na jiki da ke ba da wannan umarni?
Abin mamaki shi ne, ba cikin mutum ba ne ke sarrafa amai, kwakwalwa ce.
Amai (Vomiting ko Emesis) wata kariya ce ta halitta da Allah Ya sanya a jikin mutum. Lokacin da jiki ya gano cewa akwai wani abu da zai iya cutar da shi, sai kwakwalwa ta ba da umarnin a fitar da abin da ke cikin ciki ta baki domin kare jiki. Wannan shi ne abin da muke kira amai.
INA AKE SARRAFA AMAI?
A cikin ƙananan ɓangaren kwakwalwa (Brainstem), musamman a Medulla oblongata, akwai cibiyoyin jijiyoyi da ke sarrafa aikin amai.
Waɗannan cibiyoyi suna karɓar saƙonni daga sassa daban-daban na jiki. Idan s**a gano cewa akwai haɗari, sai su haɗa dukkan matakan da ake buƙata domin jiki ya yi amai.
TA YAYA JIKI YAKE GANO CEWA YA KAMATA A YI AMAI?
Jiki na iya aika saƙon haɗari zuwa kwakwalwa ta hanyoyi daban-daban.
1. CIKI DA HANJI
Idan abinci ya lalace, yana ɗauke da guba, ko kuma ya yamutsi bangon ciki ko na hanji, jijiyar Vagus nerve tana aika saƙo zuwa kwakwalwa cewa akwai matsala.
2. JINI
Akwai wani yanki na kwakwalwa mai suna Area Postrema, wanda ake kira Chemoreceptor Trigger Zone (CTZ). Wannan yanki yana iya gano magunguna, guba, ko wasu sinadarai masu yawo a cikin jini.
Shi ya sa wasu magunguna, musamman magungunan da ake amfani da su wajen magance cutar daji (Chemotherapy), wasu ƙwayoyin magani, ko yawan shan barasa/giya kan haddasa amai.
3. KUNNIN CIKI (INNER EAR)
Lokacin tafiya akan abin hawa misali; mota, jirgi, ko jirgin ruwa, wani lokaci abin da idanu suke gani ba ya dacewa da abin da kunnin ciki yake ji. Wannan rashin daidaiton na iya sa kwakwalwa ta ɗauka cewa akwai matsala, ta kuma tayar da amai. Wannan shi ake kira Motion Sickness.
4. TUNANI DA JI
Tsananin tsoro, damuwa, tashin hankali, wari mai muni, ko ganin wani abu mai tayar da hankali su ma na iya kunna cibiyar amai da ke cikin kwakwalwa.
ME KE FARUWA KAFIN AMAI?
Kafin amai ya fito, jiki yana yin wasu shirye-shirye:
1. Mutum yana fara jin tashin zuciya (Nausea).
2. Ana ƙara fitar da miyau domin kare haƙora daga acid da ke cikin amai.
3. Numfashi yana ɗan tsayawa na ɗan lokaci domin kada amai ya shiga cikin huhu.
4. Mashigar ciki zuwa hanji tana rufewa, yayin da mashigar maƙogwaro ke buɗewa.
5. Tsokokin ciki da tsokar da ta raba ƙirji da ciki (Diaphragm) suna matsewa da ƙarfi, suna tura abin da ke cikin ciki sama ta maƙogwaro har ya fito ta baki.
Dukkan waɗannan matakai suna faruwa cikin daƙiƙu kaɗan cikin tsari mai ban mamaki.
MEYASA MATA MASU CIKI SUKE YAWAN AMAI?
A farkon watannin ciki, jikin mace yana samar da wani sinadari mai suna Human Chorionic Gonadotropin (hCG) da yawa, tare da samun wasu canje-canjen Hormones.
Waɗannan canje-canjen kan sa cibiyar amai da ke cikin kwakwalwa ta ƙara zama cikin shiri. Saboda haka, ko ƙananan abubuwa k**ar wari, wasu nau'ukan abinci, ko wasu ƙamshi da a da ba sa tayar da amai, yanzu kan iya haddasa tashin zuciya (Nausea) da amai (Vomiting).
Ana kiran wannan yanayi Morning Sickness, duk da cewa ba lallai sai da safe kawai yake faruwa ba.
SHIN AMAI YANA DA AMFANI?
Eh. A mafi yawan lokuta, amai wata muhimmiyar kariya ce ta jiki.
Yana taimakawa wajen fitar da abubuwan da ka iya zama masu cutarwa kafin su ƙara shiga cikin jiki.
Sai dai idan amai ya yi tsanani ko ya daɗe, yana iya haifar da:
1. Rashin ruwa a jiki (Dehydration).
2. Raguwar muhimman sinadarai a jiki, k**ar Sodium da Potassium.
3. Lalacewar maƙogwaro sak**akon acid da ke cikin amai.
4. A lokuta masu tsanani, har ma da tsagewar maƙogwaro.
Abinda ya fi shi ne a gaggauta garzayawa asibiti da zarar amai ya ɗauke ɗan lokaci bai tsaya ba.
ABIN DA YA KAMATA MU SANI
Mutane da yawa suna tunanin cewa cikin mutum ne yake haddasa amai. Amma a gaskiya, kwakwalwa ce ke tsara wannan aiki tun daga farko har ƙarshe.
Tana tattara bayanai daga ciki, hanji, kunnen ciki, jini, da sauran sassan jiki. Idan ta gano cewa akwai abin da zai iya cutar da mutum, sai ta ba da umarnin a yi amai domin kare jiki.
Saboda haka, amai ba cuta ba ce a mafi yawan lokuta. Alama ce da ke nuna cewa jiki yana ƙoƙarin kare kansa daga wani abu da zai iya cutar da shi.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya halicci jikin mutum cikin tsari mai ban mamaki. Duk wata kariya da jiki ke yi tana nuna hikima da AHMAD A ASLAM