The Physical Therapist

The Physical Therapist Evidence-based women's health physiotherapy, pain management, education, and advocacy. Helping Women Move Beyond Pain.

21/07/2026
Mata da yawa suna ɗaukar ciwo a matsayin wani ɓangare na rayuwa. Amma idan ciwo ya yi tsanani, ya daɗe yana ci gaba, ko ...
09/07/2026

Mata da yawa suna ɗaukar ciwo a matsayin wani ɓangare na rayuwa. Amma idan ciwo ya yi tsanani, ya daɗe yana ci gaba, ko yana hana ki gudanar da harkokin yau da kullum, bai kamata ki yi shiru da shi ba.

A wasu lokuta, akwai hanyoyin magance ko rage irin waɗannan ciwukan. Mataki na farko shi ne fahimtar abin da ke faruwa da kuma neman shawarar ƙwararren ma'aikacin lafiya.

A SALMAI, muna da burin ilimantar da mata domin su fahimci jikinsu, su kula da lafiyarsu, kuma su rayu cikin walwala.

💬 Tambaya: Shin akwai wani ciwo da kika taɓa ɗauka a matsayin "abu na al'ada", amma daga baya kika gano cewa yana buƙatar kulawa?

Muna maraba da ra'ayoyinku a sashin sharhi.

SALMAI Muna taimaka wa mata su shawo kan ciwo domin su rayu cikin walwala.

08/07/2026

💙 Barkan ku da zuwa SALMAI
Muna taimaka wa mata su shawo kan ciwo domin su rayu cikin walwala

A kowace rana, mata da yawa suna rayuwa da ciwo suna zaton abu ne na 'al'ada'.

Ciwo lokacin daukar ciki.
Ciwo bayan haihuwa.
Ciwon ƙashin ƙugu.
Ciwon baya.
Kwacewar fitsari ba da son rai ba
Ciwon al'ada mai tsanani.

Sau da yawa akan cewa mata:
"Ai haka yake."
"Ki daure kawai."
"Zai wuce da kansa."
Amma gaskiyar magana ita ce, ba duk wani ciwo ba ne ya kamata mace ta rayu da shi. Da dama daga cikin waɗannan matsalolin ana iya tantance su, a yi musu magani, kuma a samu sauƙi ta hanyar fisiyoterapi da sauran hanyoyin da s**a dace.
A matsayina na fisiyoterapist, na ga yadda ciwo ke shafar rayuwar mace; lafiyarta, aikinta, iyalinta da kuma kwarin gwiwarta.

Saboda haka aka kafa SALMAI.
Kungiyar SALMAI za ta himmatu wajen wayar da kan mata ta hanyar bayanan lafiya masu inganci da suke dogara da hujjojin kimiyya, domin mata su fahimci jikinsu kuma su yanke shawara mai kyau game da lafiyarsu.

A wannan shafi za ku samu bayanai game da:
💙 Lafiyar Mata
💙 Lafiyar Ƙashin Ƙugu (Pelvic Health)
💙 Lafiyar Mata Lokacin Juna Biyu da Bayan Haihuwa
💙 Motsa Jiki
💙 Abin da ake cewa da abin da gaskiya ta nuna game da lafiyar mata

Ko kina neman ilimi, shawara, ko hanyoyin da za su taimaka miki domin ki rayu cikin ƙoshin lafiya, da yardar Allah za ki samu hakan a SALMAI.
Wannan ba shafi ba ne kawai.
Kungiya ce da aka gina domin taimaka wa mata su fahimci jikinsu, kuma su rayu cikin ƙoshin lafiya.

Barkan ki da zuwa SALMAI.
Muna taimaka wa mata su shawo kan ciwo domin su rayu cikin walwala.

08/07/2026

💙 Welcome to SALMAI; a new chapter of The Physical Therapist

Helping Women Move Beyond Pain.

Every day, many women live with pain that they believe is "normal."
Pain during pregnancy.
Pain after childbirth.
Pelvic pain.
Back pain.
Urinary leakage.
Painful periods.
Too often, women are told:
"It's normal."
"Just endure it."
"It will get better with time."
But while some discomforts are common, many painful conditions can be assessed, managed, and improved with the right care.
As a physiotherapist, I have seen how pain can affect a woman's confidence, her family, her work, and her quality of life.

That is why SALMAI was created.
SALMAI is committed to providing evidence-based education on women's health , pain management, and movement, so that every woman can make informed decisions about her health.
Here, you'll find content on:
💙 Women's Health
💙 Pain Management
💙 Pelvic Health
💙 Pregnancy & Postpartum Care
💙 Exercise & Movement
💙 Physiotherapy Myths & Facts

Whether you're looking for answers, support, or practical health information, you're welcome here.

This is more than a page.
It is the beginning of a community dedicated to helping women understand their bodies, move with confidence, and live healthier lives.

Welcome to SALMAI.
Helping Women Move Beyond Pain.

09/09/2024

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when The Physical Therapist posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share