04/06/2026
KU SHAQATA DA WANNAN
Wata budurwa ce muka hadu da ita a nan facebook, mun saba da ita ta inbox sosai, to irin yan matan nan ne da basa saka hoton su domin nayi yawon duniya a profile ɗinta banga hoton ta ba... Sai nace ta turo mini hoton ta na gani tunda dai yanzu mun riga da mun saba da juna...
Tace to, nan take ta turomin hotuna uku, (kasan al'adanmu ta samari da kuranta mata ko basuda kyau, su kuma al'adan mata son yabo ko basu cancanci yabon ba)...Don a halayya ta mace zata iya zama dakai ko ba Abinci indai kana kuranta ta, Nan fa na fara typing ina yabo da kurantata, sai da nai minti sha biyar ina yabata kannan na tura sakon yabona...🥴
"Gaskiya kin hadu, idanunki farare kamar madara, gasu daƙwa-daƙwa kamar kinsha Codyn, gashin girarki masu kyau sun lankwashe a saman idanunki... Gabakin dan karami kamar gidan tsutsa, wuyanki siriri kamar mariƙin lema, gaki da shape kamar kalangu...."😂
Da taji wannan baituka sai tace, Wallahi bani bace bari kaga hotona, sai ta turomin wasu hotunan na daban, tace Wallahi wannan sune hotunana waccan ƙawatace Raheelah...
Sai na fahimci yabon nan ne takeso na dawo dashi kanta, ni kuwa sai na tsaya bisa ga kafafuna nace Allanbaran sai ta bani number Raheelah ni itace tayi mini... (Kuma a batu na gaskiya tafi Raheelan kyau da komi)...
Karshe dai ranta ya baci ta daina kulani, yau mako daya kenan kullum da karfe takwas na safe sai na tura mata sakon, "Ina Raheelah ta,
Wacce mata s**a rakota Duniya don tsabar kyawunta?" 😂..... Shiru babu reply.
Ni na tsani abun haushi Idan bani zanyi ba, Nafiso idan na tambayi mutum ya faɗamini gaskiya ko zai mutune ni ban damu ba, burina kawai ya faɗan gaskiya.😠
Daka bani labarin gaskiya nayi dariya, gara ka bani labarin karya nayi kuka yafiye min sauki.🥴