07/08/2024
Soyayyar Annabi MUHAMMADU ita ke saita zuqata,suyi kyau,ita ke haskaka Mai ita I zuwa hasake masu girma ya keta hijabai na jalala da jamala har I zuwa K**ala Mai girma,domin son Annabi MUHAMMADU baya bari mutum yai Wasa da Allah ko sha'aninsa komai zai doru akan saitine saboda Annabi MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.
Kaso Annabi MUHAMMADU yakai Dan uwa da dukkan rayuwarka,kayi haquri da cutarwar mutane domin Dole itace sinadarin da ake takawa zuwa matsayai masu daraja,so akeyi kamanta kowa har kanka,ya zamana baka gane Mai sonka ko maqiyinka ka narke cikin hadarar Annabi MUHAMMADU kurum kana Mai biyayya da sallamawa zuwa gareshi zahiri da badini.
Ka kula da Sha'anin soyayyarka ka dinga duba zuciyarka Yaya gudun taraqinka yake,cikin soyayya shi yasa aka so kasamu wani daga cikin cikin almajiran sufaye shaihi Mai izini sahihi da zai dinga cilla haskenka I zuwa sama,daka zo talalabiya bazata samekaba albarkacinsa saboda suna da izini Mai girma daga hadara,musamman idan ya Zama Almajirin Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim R.T.A to tabbas soyayyarka zata tafi zuwa sama.
Duk girman maqiyanka mantasu kurum lokacinka Mai tsadane ka yawaita istigfari da salatin Annabi MUHAMMADU,Babu maganar Wasa da Ibada,kayi karatu iya iyawarka,Wanda yaganka akan hanya yaima magana ku gaisa,Wanda ya Kau dakai qyaleshi kayi sha'aninka Kai da ke fadar Annabi MUHAMMADU Mai tsarki inda shehu Tijjani yake Mai zai dameka?ka kula kayita salati istigfari yakama bakinka,shi Kuma salati ya K**a zuciyarka da ruhinka,Babu K**ar Manzon Allah mu riqeshi muyita tafiya komai zai samu albarkacinsa SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM πππ.