Sarkin Aska Modern Cupping & Traditional Medicine Venture

Sarkin Aska Modern Cupping & Traditional Medicine Venture Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sarkin Aska Modern Cupping & Traditional Medicine Venture, Medical and health, Near Wudil General Hospital Kano, Wudil.

Wannan Shafi yana gabatar da Ayyukan mu ne na wanzanci da magungunan Gargajiya a zamanan ce dan sanar da Al'umma iron cigaban da ake samu a sana'ar tare da gabatar da irin magungunan mu ga mai bukata.

29/05/2026
25/05/2026

1524 likes, 123 comments. “ ”

Herbal medicine preparation, packaging, and leveling in modern methods by Diploma Students
24/05/2026

Herbal medicine preparation, packaging, and leveling in modern methods by Diploma Students

Muna Gabatar muku DA makarantar ilmin duba lafiya ta GARGAJIYA A ZAMANANCE a Wudil JIHAR KANO. an fara sai da form GA ma...
18/04/2026

Muna Gabatar muku DA makarantar ilmin duba lafiya ta GARGAJIYA A ZAMANANCE a Wudil JIHAR KANO. an fara sai da form GA masu bukata, a WUDIL KAN HANYAR GAYA DAIDAI KWANAR ASIBITI, SHAGON DEPUTY BUSINESS CENTRE.

05/04/2026

Allah Gwani | Abubuwan Mamaki 11 Game Da Ƙwaƙwalwa.

1] A yayin da ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa, wato "brain cells", a wani sashi s**a mutu, na wani sashin na iya karɓar aikinsu. Wannan shi ne abin da ke faruwa a ƙwaƙwalwar mai shanyewar ɓarin jiki har motsin hannu ko ƙafa su dawowa bayan shanyewarsu.

2] Ƙwaƙwalwa ba ta ɗauke da maganaɗisan jin ciwo, wato "pain receptors", saboda haka, ƙwaƙwalwa ba za ta iya jin ciwo kamar yadda sauran sassan jiki ke jin ciwo ba. Saboda haka, ciwo daga kai na zuwa ne daga sauran sassan da ke kewaye da ƙwaƙwalwa, amma ba ƙwaƙwalwar kanta ba.

3] Ƙwaƙwalwa ta fi kowane sashin jiki son kanta. Domin duk da cewa nauyinta ba ya wuce kaso uku cikin ɗari (3%) na nauyin jikin mutum, amma dole sai an ba ta kaso talatin cikin ɗari (30%) na yawan jinin da zuciya ke turawa a kowane bugu.

4] A mafi yawan lokuta, ɗan Adam na amfani da dukan sassan ƙwaƙwalwarsa, saɓanin tatsuniyar da ke cewa wai ɗan Adam na iya amafani da ɗan wani sashi na ƙwaƙwalwarsa ne kawai a tsawon rayuwarsa.

5] Kimanin rabin sinadaran abincin da yara ke ci suna tafiya ne wajen gina ƙwaƙwalwarsu domin koyo.

6] Kamar yadda motsa jiki ko atisaye ke ƙara lafiyar jiki, haka ma yake ƙara lafiyar ƙwaƙwalwa.

7] Kamar yadda tambarin babban yatsan hannunka (thumbprint) yake daban da na kowa, haka ma yadda ƙwaƙwalwarka ke aiki daban da ta kowa.

8] Saboda ƙwaƙwalwa na aiki ne da tsarin lantarki, a yayin da mutum yake a farke, ƙwaƙwalwa na iya samar da ƙarfin lantarkin da zai iya kunna farin ƙwan lantarki.

9] Kimanin kaso sittin cikin ɗari (60%) na ƙwaƙwalwa kitse ce.

10] Rashin isashshen bacci na rage kaifin ƙwaƙwalwa. Ɗan Adam yana buƙatar baccin kimanin awanni bakwai zuwa tara a kullum.

11] Ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa ba sa iya jure rashin iskar oksijin da sida(gulukos) na fiye da mintina biyar face sun mutu.

© Physiotherapy Hausa

Address

Near Wudil General Hospital Kano
Wudil

Telephone

+2348172333323

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sarkin Aska Modern Cupping & Traditional Medicine Venture posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sarkin Aska Modern Cupping & Traditional Medicine Venture:

Share