23/01/2026
Dental Caries (Ciwon Hakori / Ruɓewar Hakori)
Menene kogon Hagori (Dental Caries?)
Kogon Hakori (Dental caries) cuta ce da take sa hakori ya ruɓe ko ya samu rami, sakamakon ƙwayoyin cuta da suke amfani da sukari su samar da acid wanda ke lalata hakori a hankali.
Me ke jawo shi?
🦷 Cin abubuwa masu sukari da yawa
🦷 Rashin wanke hakori yadda ya kamata musamman da dare
🦷 Shan kayan zaki akai-akai
🦷 Rashin zuwa duba hakori lokaci-lokaci
📍Alamomi:
🔹 Zafi yayin cin abu mai sanyi ko zafi
🔹 Rami ko baki a hakori
🔹 Warin baki
🔹 Ciwon hakori mai tsanani
💊Magani:
🦷Filling (cike rami) idan anje Assibiti da wuri
🦷Root canal idan ya ciwon ya tsananta
❌Cire hakori idan ya lalace baki daya
💉Rigakafi:
✔️ 🦷☃️ Wanke hakori sau 2 a rana da man goge mai fluoride
✔️ 🍹 Rage cin sukari
✔️ 🪥 Amfani da asawaki ko floss
✔️ 🏥 Zuwa duba hakori akai-akai
Akiyaye Riga kafi yafi Magani
Malami Yabo Rchp